Katsina: Gwamnatin Tarayya Ta Bada Tallafi Ga Matan Karkara

A kokarinta na rage radadin da cutar Korona ta jefa al’umma, akalla matan jihar Katsina, dubu shidda da dari takwas ne, za su amfana da tallafin naira dubu ashirin kowanen su, wanda aka zabo daga matakin mazabu dari ukku da sittin da daya da ke jihar Katsina.

Ministan Jin Kai Da Kare Afkuwar Bala’o’i, Hajiya Sa’adiyya Faruq ce ta bayyana haka, a lokacin da ake kaddamar da bada tallafin a gidan gwamnati jihar Katsina a yau laraba.

Ministan ta bayyana cewa, a kokarin gwamnati Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na tallafawa al’umma, musamman masu karamin karfi, Shugaban Kasa Buhari ya bada a kawo maku, ni ‘yar aike ce kurum, Saboda yadda ya damu da mawuyacin hali, da halin da cutar Corona ta jefa su, ya ga ya dace a tallafawa talakkawan kasar nan, tun da muka hau gwamnati a tsaye take wajen ganin ta fitar da talakkawa wannan hali, mun kirkiro shirye-shirye da dama, karkashin wannan Ma’aikata. Zuwa yanzu jihar Katsina a wadannan shirye-shirye, ta sama da miliyan dubu tara, domin rage fatara a jihar Katsina. Wannan shiri ne na tallafawa mata na karkara, su dubu shidda da dari takwas.

Da yake jawabi, mataimakin Gwamna jihar Katsina, Alhaji Mannir Yakubu, ya bayyana jin dadinsa, bisa ga wannan tallafi da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kawo wa matan jihar Katsina, muna mika sakon godiyarmu ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Ministan Jin Kai, a madadin wadanda za su amfana da tallafin. Ina kira ga al’ummar da za su amfana da shirin, da su yi amfani da shi ta hanya mai kyau.

Labarai Makamanta