Da yammacin ranar Juma’ah ne wani munnan lamari ya faru a Unguwar Gafai cikin Birnin Katsina wanda ya saka mutane cikin juyayi da kuka na rasuwar wata baiwar Allah mai suna Fateema Junaidu, ta bar gidan mijinta zuwa Unguwar domin taya wata daga cikin Aminan arziki murnar samun karuwa, ma’ana taje bikin suna.
To dayake a Unguwarsu ake sunan wajen gidan mahaifanta, daga gurin sunan taje gidansu domin gaishe da mahaifiyarta, da sauran danginta dake cikin gidan dama yankin Unguwar baki Daya, saboda mafi yawan yan Unguwar ‘Yan’uwan juna ne.
Ta aje diyarta mai suna Fatima a cikin gida, ta fito waje suna gaisawa da abokan arziki, taya tsaye ta bada baya, wani tsohon bango a gidansu ya rufto mata, nan take aka dauketa zuwa Asibitin Kwararru na Jahar Katsina, ta samu kara a cinyoyida da hannuwa harma kashin hannunta guda ya fito, da zuwa Asibitin ba’a wuce mintuna Ashirin ba tace ga garinku nan.
Wannan lamarin ya jefa mutane cikin zullumi da mamakin ganin cewa lafiayarta kalau, kowa yaji rasuwar Fatima sai ya yi mamaki tare da tunanin abubuwan alkhairi da take da su, fatima ta rasu shekaru biyu da wata daya da auranta, ta rasu ta bar mijinta Muhammad Rabiu Gafai da diyarta Fatima.
Da nake zantawa da mijinta game da dabi’unta ya sheda min cewa “lallai Fatima ta kasance mai hakuri da tausayi, domin duk abunda ya shafeni ko ita na kudi taya iya kanta saboda tana yin dinki kuma tana samun alkhairi, nayi rashin farin cikina abun kaunata, ina addu’a Allah Ya gafarta mata, ya kasance tare da ita ya bamu hakurin rashi baki Daya, domin rashin Fatima rashi ba ni kadai ba, domin yadda mutane kadai suna taru zakasan cewa lallai Fatima ta samu sheda da yabo yadda take sakin fuska da walwala ga kowa”.
Da wannan muke miko sakon ta’aziyya ga al’ummar Unguwar Gafai da dama musulmi baki daya, muna kuma nema da barar addu’ionku akan wannan rashin.