Katsina: Dakarun ‘Yan Sanda Sun Hallaka ‘Yan Bindiga

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ne ya sanar da hakan a cikin wani jawabi da aka rabawa manema labarai a Katsina.

Ya bayyana cewa an samu wannan nasara ne yayin da jami’an rundunar ‘yan sanda a karkashin atisayen ‘Puff Adder’ su ka dira yankin bayan samun rahoton bullar ‘yan bindiga dauke da makamai.

A cewarsa, rundunar ‘yan sanda ta samu labarin cewa ‘yan bindiga dauke da bindigogi samfurin AK 47 sun shiga kauyen Kwaro da ke yankin karamar hukumar Dutsinma a ranar 12 ga watan Agusta. SP Isa ya kara da cewa ‘yan bindigar sun kashe wani mutum mai suna Mohammed Auwal tare da sace wasu mutane biyu da dabbobi ma su yawa.

Kakakin ya bayyana cewa an yi musayar wuta a tsakanin ‘yan bindigar da kuma jami’an rundunar ‘yan sanda da su ka bi sahunsu a lokacin da su ke kokarin tserewa.

Ya ce jami’an rundunar ‘yan sandan sun samu nasarar kashe biyu daga cikin ‘yan bindigar yayin da sauran abokansu su ka gudu zuwa cikin daji tare da barin babura guda bakwai.

“Mun kubutar da mutane biyu; Musa Rabiu da Rabiu Sani, daga hannun ‘yan bindigar ba tare da ko kwarzane ya samesu ba,” a cewarsa.

Kazalika, ya bayyana cewa rundunar ‘yan sanda ta samu nasarar wani kwanson alburusan AK 47 guda daya da ‘yan bindigar su ka jefar sakamakon matsin lambar da su ka fuskanta a wurin jami’an ‘yan sanda.

SP Isa ya ce har yanzu jami’an ‘yan sanda sun kewaye dajin da ‘yan bindigar su ka shiga domin zakulo gawarwakinsu ko kuma kashesu idan suna raye.

Labarai Makamanta

Leave a Reply