Binciken da rundunar ‘yan sandan Najeriya ta yi a Katsina ya gano cewar, yara 5 da suka mutu da safiyar ranar asabar 18 ga watan Yuli bayan fashewar wani abu a gona, sun tsinci bam din gurnetin sojoji ne, wanda suka rika wasa da shi, ba tare da sun san ko menene ba.
Kakakin rundunar ‘yan sandan a Katsina SP Gambo Isa ne ya sanar da sakamakon binciken da suka gudanar kan lamarin da ya auku a kauyen Yammama dake karamar hukumar Malumfashi.
A baya dai mazauna yankin sun ce mutane 6 suka mutu, sai dai rundunar ‘yan sanda ta jaddada cewar mutane 5 suka rasa rayukansu, dukkaninsu ‘ya’ya ga wani Alhaji Adamu.
Bayanai sun ce yaran 11 da lamarin ya rutsa da su sun je gona ne domin yin ciyawar dabbobi.
Katsina na daga cikin jihohin arewacin Najeriya masu fama da matsalar hare-haren ‘yan bindiga dake halaka rayukan jama’a, da kuma satar mutanen don karbar kudin fansa.
A baya bayan nan ne kuma dakarun sojin Najeriya na sama da na kasa sun kaddamar da sabbin hare-haren murkushe ‘yan bindigar dake addabar jama’a a yankunan arewa maso yammacin kasar.