Katsina: An Gudanar Da Jana’izar Mutane 15 Da ‘Yan Bindiga Suka Kashe

Da safiyar yau Talata ne, Sarkin Ruman Katsina, Hakimin Batsari, Alhaji Tukur Mu’azu Ruma ya jagoran jana’izar, mutane goma Sha biyar da Yan Bindiga Suka Kashe a kauyen Yar Gamji da ke Kan aiki a gonakin su da safiyar jiya litinin.

Wakilimu ya samu halattar Sallar Jana’izar da aka gudanar a farfajiyar babban asibitin garin Batsari, da Misalin karfe goma na safiyar yau, Wanda babban limamin garin Batsari, Liman Ishaqa Batsari ya jagoranta.

Mutanen masu mabanbanta shekaru an rufe su a makabartar Magama da ke cikin garin Batsari da Misalin karfe goma da rabi aka kamalla rufe su. Jana’izar ta samu halattar al’ummar garin da Kuma Danmajalisar Mai Wakiltar karamar hukumar Batsari, Jabiru Yauyau.

Wani abu da wakilinmu ya lura da shi, shi ne gawarwakin sun kwana a asibitin, a kasa babu wajen aje gawarwaki a asibitin ta Batsari. Kuma ta hango wasu daga cikin mata da iyayen wadanda aka kashe suna ta sharbar kuka a cikin asibitin garin Batsari inda anan ne gawarwakin suka kwana. Al’ummar Karamar Hukumar Batsari, sun yi kira ga Gwamnatin Jihar Katsina da ta Tarayya da suka kawo masu dauke, kullum sai sun zo sun kashe mu.

Allah ya jikansu da rahama

Labarai Makamanta

Leave a Reply