A kalla mutum 50 aka garzaya da su babban asibitin da ke garin Rimaye na karamar hukumar Kankiya ta jihar Katsina domin ceto rayukan su.
Hakan ya biyo baya ne sakamakon cin abinci a wajen wata walima da aka yi a yankin, ana zargin guba jama’ar suka ci a cikin abincin walimar.
Ko a kwanakin baya a yankin ?aramar hukumar Batsari ta jihar Katsina an samu irin wannan matsalar inda wani Saurayi ya ha?a baki da Budurwarshi suka zuba guba cikin tukunyar abincin biki, lamarin da ya kai ga rasa rayukan wasu bayin Allah.
Wannan muguwar ?abi’a ta zuba guba cikin abincin biki ko na walima na nema zama ruwan dare a jihar Katsina da sauran jihohin Arewa, inda ake samun wasu ?ata gari suna fakon idanuwan Mutane suna zuba guba cikin abinci da abin sha.
Muna fatan bayin Allah wa?anda suka gamu da wannan iftila’in Allah zai basu sauki da waraka, muna kuma fatan Allah ya sa ayi nasarar kama wa?anda ke da hannu a wannan aika aikar domin fuskantar hukunci.