Katsina: An Damke Tsohon Da Ya Ƙware Wajen Lalata Da Yara

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina, karkashin jagorancin kwamishinan ‘yan sanda, Sanusi Buba ta yi nasarar cafke dan shekara hamsin da daya, Jabiru Audu, dake zaune a unguwar Tudun Yan Lihidda, cikin garin Katsina da ya kware wajen lalata kananan yara.

Jabiru Audu ya amsa laifinsa kuma bai son ko Sau nawa ya yi lalata da su ba, yana ba su naira hamsin zuwa dari. An zo da yara hudun da yake lalata da su a gidan wata Inna Haja, mai kosai, idan ta tafi tallar kosai.

Daga Jamilu Dabawa, Katsina

Labarai Makamanta

Leave a Reply