Katsina: An Damƙe Matar Da Ta Yi Garkuwa Da ‘Yarta Ta Nemi Kuɗin Fansa

Wata Matar Aure, Ta Sache Diyarta Ta Boye da sunan an Sache ta, Domin Tayima Bazawarar Mijinta ‘Kazafin Satar a Jahar Katsina…

Kishi za’a Kira wannan Abun komi Rundunar Yansandan Jahar Katsina sunyi Nasarar Chafke wata Mata Mai suna Fatima Bishir, Yar Kimanin Shekaru 22 dake Unguwar Sabon Layi a Karamar Hukumar, Mashi dake Jahar Katsina wadda ta kitsa yadda aka sache Yarta Yar Kimanin Shekaru Biyar Mai Suna Fatima Bishir, domin neman kudin Fansa.

Ita dai Wannan Matar tayi haka ne domin ta jama Zawarar Mijin nata Mai Suna Aisha Musa Yar Kimanin Shekaru Ashirin da Biyu, Sharri domin a zargeta da Sache Diyar Bazawarin nata.

Yayin da Jami’an Tsaron suka matsa da Binchike wadda ake zargin ta amsa Laifinta kamar haka:

A ranar 5/07/2020 da Misalin karfe 0800hrs, taje Offishin Yansanda dake Mashi Division takai Rahoton bachewar Yarta Mai suna Fatima Bishir, ‘yar Kimanin Shekaru 5 tareda bada Tabbachin cewa tana zargin Tsohuwar Matar Mijinta wadda yake shirin dawowa da ita, itache ta sache mata ‘Ya, tama yi zargin cewa Aisha ta taba yimata Barazanar cewa Matsawar ta dawo Dakin Mijinta sai ta rama kisan Diyarta da ta Mutu a Hannun ta.

Fatima tayi kokarin kauda Hankali Jami’an tsaro ta hanyar sanya kayan Diyarta Fatima da ta bata a Gidan Aisha Musa Inda Jami’an tsaron Yansanda suka wando da Takalmin canvas ‘Yar da ta bache duk dan ta bata mata suna.

Ta kuma Bayyana yadda ta Aikewa Mijin nata sakon waya tareda barazanar cewa yabiya kudin fansa Naira Milyan Biyu ko kuma za’a kashe’Yar tashi.

Ta kuma Bayyana yadda ta sake akewa da wani sakon zuwa ga Yayan Jawarar Mijin nata Sani Musa, da Tsohon Mijinta Auwalu Haliliu, wanda kafi sani da “Al-Jazira” Inda take zargin su day cewa sune suka hada baki wajen sache ‘Yar tata.

Ta kuma Bayyana yadda ta dauki Diyarta ta zuwa Jahar Kano ta hanyar taimakon wata Fa’iza Yar Aikin Gidan ta duk a Yunkurin ta na Tabbatar da Cewa an sache mata ‘Ya.

Jami’an tsaro kuma Sunyi Nasarar Chafke Faiza a Karamar Hukumar Dutsi inda take kokarin ajiye ‘Yar a gaban Gidan Mahaifiyar Aisha mai suna Dije duk dai a kokarin su na Lallai sai sun nuna cewa Aisha Musa itach ta sache ‘Yar.

Jami’an tsaro suna Chigaba da Binchike akan Lamarin.

Labarai Makamanta

Leave a Reply