Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Katsina: An Damƙe Matar Da Ta Azabtar Da Ɗan Riƙo

Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Katsina, karkashin jagorancin Kwamishinan ‘yan sanda Alhaji Sanusi Buba, ta yi nasara kama Malama Rahama Sani, yar shekara arba’in da biyar da ke zaune a Unguwar Kwado, cikin garin Katsina, wadda ake zargi da muzgunawa da cin zarafin, Abdulkadir Muawiyya, dan shekara shidda da mahaifinsa ya kai shi riko a hannun ta sakamakon rabuwa da mahaifiyarshi.

Jami’in hulda da Jama’a, na rundunar ‘yan sanda ta Jihar Katsina SP Gambo Isah ya bayyana haka, lokacin da ake baje-kolin masu laifi a helkwatar rundunar da ke Katsina.

SP Gambo Isah ya kara da cewa an samu Abdulkadir Muawiyya, da raunuka daban daban a jikinsa, ciki har da kariya, wanda muka kaishi asibiti aka gyara mashi. Duk sadda yaron nan ya ji muryarta zai kwartsa ihu, saboda gilla da ta gasa mashi. Muna kuma cigaba da binciken.

Shima mahaifin yaron Malam Mu’awiyya, ya shaidaiwa wakilinmu cewa wani aminin shi ne ya hada shi da Malama Rahama, ya rabu da mahaifiyarshi, shi ne ya kai Mata shi ajiya yau, kusan wata hudu kenan, duk lokacin na yi kokarin kiranta, ta waya ba ta dauka ko kuma ta ce ba ta gari, haka ta yi boye man, har Allah ya sanya wata kungiya kare hakkin Yara, ta yi nasarar ceto dan nawa tare da taimakon yan sanda.

Ita ma wadda ake zargin, Malama Rahama ta bayyana wakilinmu cewa ni mahaifin shi ya kawo man shi, ya ce in taimake shi in rike mashi shi, sakamakon rabuwa da mahaifiyarshi, ya auri wata matar ta ce ba za ta zauna da shi ba, ko lokacin da ya kawo shi akwai tabunna na raunuka ga yaron, kuma ni ban so yanke mashi mazakuta ba, mai kaciya ya zo, ya kama ihu na ce a kyale shi, domin mu sanya shi makaranta, ruguwar da ya yi ya Fadi, ya samu tsagewar kashi, sai kuma ruwa zafi da ya fada, a lokacin da ake mashi.

Wani abu da wakilinmu ya lura da shi, duk yadda Allah ya yi jikin yaron rudu rudu yake na sawon bugu a koina, haka mazakuta Abdulkadir Muawiyya, dan shekara shidda akwai sawun yanka kuma ba wurin da ake kaciyar ba, ga alama an so yanke ta. Kafarsa ta dama nannade take da bandaje, ga tabunna raunuka daban daban a koina a jikinsa.

Exit mobile version