Katsina: An Damƙe Masu Lalata Da Ƙananan ‘Yan Mata

Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Katsina karkashin jagorancin Kwamishinan yan sanda Sanusi Buba ta yi nasarar cafke wadansu magidanta wadanda ake zargin da lalata da wadansu kananan yara a Katsina.

Mai magana da yawun rundunar’yan sanda ta jihar Katsina, SP Gambo Isa ya baje kolin su ga manema Labarai a helkwatar rundunar da ke Katsina.

Gambo Isah ya kara da cewa wadanda rundunar ta cafke akwai Rabilu Abubakar, dan shekara talatin da haihuwa da Iliyasu Ya’u, dan shekara hamsin da daya da Abubakar Magaji, dukkansu mazauna Unguwar Yari cikin birnin Katsina da kuma Musa Abubakar, dan shekara arba’in da Ukku da yake zaune a Unguwar Madawaki, cikin birnin Katsina.

SP Gambo Isah ya ce sun yi luwadi da wadansu yara guda biyu, Musa Ibrahim, dan shekara sha shidda da kuma Abdulrashid Ibrahim, dan shekara sha ukku. Inda suke daukar su suna kai su kango da shaguna suna lalata da su.

Gambo Isah ya ce dukkan su sun amsa laifin su.

Labarai Makamanta

Leave a Reply