Shugaban kwamitin tsaro na jihar Katsina, kuma sakataren gwamnati jihar Katsina, Alhaji Mustapha Muhammad Inuwa ya roki al’umma da su dukufa yin addu’o’in samun dawammamen zaman lafiya, da kuma addu’ar Allah ya toni asirin duk wanda ke da hannu a cikin sace-sacen mutane da kashe-kashen yan bindigar ke yi a jihar Katsina dama Nijeriya baki daya.
Malam Mustapha Muhammad Inuwa, ya bayyana haka ne, a lokacin da yake jawabin bankwana ga wasu mutane talatin da bakwai da gwamnatin jihar Katsina ta kubutar a hannun yan bindiga, a sasanin ‘yan yi wa kasa hidima da ke kan hanyar Mani a cikin garin Katsina.
Dakta Mustapha Inuwa ya kara da cewa masu aikata wannan ta’addanci, akwai masu taimaka masu cikin mutanen gari, sai mu yi ta fatan Allah ubangiji ya yi mana maganin su ya kuma kawo karshen sa. Duk wanda ke da hannu a cikin wannan ta’addanci ko ta kowacce hanya, Allah ubangiji ya yi mana maganin su. Wadanda ke kokarin kullum su ga an samu zaman lafiya kamar su jami’an tsaro da masu rike da madafun gwamnati da mutanen ke addu’a a samu zaman lafiya, Allah ya ci gaba da ba mu nasara kawo karshensa a jihar Katsina da ma sauran jihohin kasar nan da ke fama da makamanciyar wannan matsalar.
Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, kuma Shugaban kwamitin tsaro ya jadadda muhimmancin yin addu’o’i, domin babu abinda ya gagari Allah. Haka zalika, ya taushi wadanda aka kubutar din, da su dauka wani mukkadari abu ne, wanda ba makuwa sai ya faru, ku yi wa Allah godiya da aka kubutar da su da ransu da Lafiya.
Daga karshe, ya ce gwamnati jihar Katsina, karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari, za ta ci gaba da yin bakin kokarin ta, na ganin tsaro ya inganta a jihar Katsina. Samar da tsaron lafiya da dukiyoyin su, hakki ne da ya rataya a wuyanmu, amma al’umma sai sun ci gaba da ba da hadin-kai, kamar yadda suka saba. Kuma gwamnan jihar, Alhaji Aminu Bello Masari, ya ba su dan hassahi na kudi da za su tafi.
Gwamnatin Jihar Katsina, cikin satin nan ta kubutar da mutane dari da arba’in, wadanda aka kubutar da su a hannun ‘yan bindiga, ta hanyar yin sulhu ba tare da sun biya kudin fansar ba. Masari ya bayyana cewa damar da muka samu ta amso daliban makarantar sakandire ta Kankara, su dari ukku da arba’in da hudu, ita ce mu ke amfani da ita, don mu ga duk wanda ke tsare hannun yan bindigar nan, mun kubutar da shi, ba ma dan jihar Katsina ba kawai, dama ce da aka samu don kar ta kucce.