Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar kula da basuka (DMO) ya gargadi gwamnatin tarayya game da kar?o ?arin bashi, inda ya bayyana cewa kashi 73.5% na kudaden shigar ?asar a bana za a yi amfani da su wajen biyan bashi.
Ofishin kula da basukan ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa bashin da ake bin ?asar na iya kai wa kashi 37.1% na jimillar arzi?in da take samu daga abin da ta sarrafa a cikin gida wato GDP a bana, daga kashi 23% da aka samu a ?arshen 2022.
Ofishin ya danganta hasashen da ake yi na hauhawar bashin da sabbin basuka da aka ciwo daga ?asashen waje da kuma wanda aka karbo daga babban bankin ?asar.
A watan jiya, Majalisar Dokokin Najeriya ta amince da wasu ma?udan ku?i da suka kai Naira tirliyan 22.7 (dala biliyan 50) daga babban bankin ?asar, kwana 30 kafin ?arewar wa’adin gwamnatin Buhari, da nufin ?ara kasafin ku?i da kuma aiwatar da ayyukan raya ?asa.
Jimillar bashin da ake bin Najeriya ya kai dala biliyan 103 (Naira tiriliyan 46) ya zuwa Disamba 2022.
Sabon shugaban kasa Bola Tinubu na fama da matsalar bashi, da karancin bunkasar tattalin arziki, da hauhawar farashi, da kuma tsadar rayuwa amma yana fatan yin sauye-sauyen da za su daidaita tattalin arzikin ?asar.