Kashe-Kashe A Arewa Sarakuna Sun Bukaci A Kawo Karshen Matsalar

Majalissar Sarakunan Arewa ?ar?ashin jagorancin mai alfarma Sarkin Musulmi Dr Sa’adu Abubakar, sun yi kiran yin dukkanin mai yiwuwa wajen kawo ?arshen kashe-kashen da ke addabar yankin Arewa cikin gaggawa.

Shugaban Majalisar Sarakunan kuma mai alfarma Sarkin Musulmi Dr Sa’adu Abubakar ya yi kiran, a yayin taron da Sarakunan yankin Arewa suka gudanar domin shawo kan matsalar tsaro a yankin, a taron da suka yi a Kaduna.

Mai alfarma Sarkin Musulmin yace abin damuwa ne da takaici yadda kisan jama’ar Arewa ya zama ruwan dare a Najeriya, kuma ba abu ba ne wanda za’a yi shiru akai dole ne a gaggauta ?aukar matakan da suka dace wajen magance matsalar.

Tun farko da yake gabatar da jawabi, mai girma Gwamnan Jihar Kaduna Nasiru El Rufa’i wanda shine mai masaukin ba?i, yace kashe kashe da ke faruwa a yankin arewa, ba abu bane mai da?in ji, kuma lalle a matsayin su na gwamnoni za suyi dukkanin mai yiwuwa wajen shawo kan matsalar.

Ya kuma bayyana matakan da gwamnatin Jihar Kaduna ke ?auka domin da?ile rikicin da ke faruwa tsakanin manoma da makiyaya a jihar, domin samar da dawwamamen zaman lafiya.

Illahirin Sarakunan Arewa daga jihohi 19 na yankin harda Birnin Tarayya Abuja sun samu halartar taron, wasu da aka zanta da su, sun bayyana muhimmancin wannan taro tare da alwashin aiwatar da matakan da suka dace a yankunan Masarautun su domin cimma nasarar da ake nema.

Related posts

Leave a Comment