Kasashen Waje: Yadda CORONA Ta Shiga Zuriyar Amitabh Bachcan

Hukumomin lafiya a jihar Maharashtra da ke India sun ce cutar korona ta kama zuri’ar shahararren dan wasan kwaikwayon kasar Amitabh Bachchan.


Sakamakon gwajin cutar da aka fitar ranar Lahadi ya nuna cewa Aishwarya Rai Bachchan, tsohuwar sarauniyar kyau ta duniya, da ‘yarta Aaradhya, ‘yar shekara takwas sun kamu da cutar korona.


Mijinta Abhishek da surukinta Amitabh, dukkansu sun kamu da cutar ranar Asabar kuma an kai su asibiti.

An ce taurarin biyu maza sun nuna alamar kamuwa da cutar.
Abhishek Bachchan ya wallafa sakon Twitter cewa suna ci gaba da zama a asibiti “har sai abin da likitoci suka yanke shawara a kai”.


Aishwarya Bachchan, mai shekara 46, na cikin fitattun taurarin fina-finan Bollywood a India da kuma kasashen waje, inda ta fito a fina-finan kasar da na Amurka da dama.

Rahotanni sun ce Aishwarya da ‘yarta ba su nuna alamar kamuwa da cutar ba. Mijinta ya wallafa sakon Twitter da ke cewa za su killace kansu a gida.
Ranar Asabar Amitabh Bachchan ya shaida wa miliyoyin masu bibiyarsa a Twitter cewa ya kamu da Covid-19.


“Na kamu da cutar korona, an kai ni asibiti, an yi wa iyalai da ma’aikata gwaji, ana jiran sakamako,” a cewarsa.
Bachchan, mai shekara 77, ya fito a fina-finai fiye da 200 a cikin shekara fiye da hamsin.

Bachchan ya lashe kyautuka da dama tun da ya soma tashe a shekarun 1970
An kai shi da Abhishek, mai shekara 44, asibitin Nanavati da ke Mumbai ranar Asabar. Abhishek ya bayyana cewa suna dauke da kananan alamomin cutar.


A halin yanzu Amitabh yana bangaren killace mutane na asibitin, a cewar kamfanin dillancin labaran ANI, wanda ya ambato mai magana da yawun asibiti. Ya bukaci dukkan mutumin da ya yi mu’amala da shi a cikin kwana 10 da suka wuce ya je a gwada shi.


Gwaji ya nuna cewa mai dakinsa Jaya ba ta kamu da cutar ba, a cewar jami’ai. Sai dai ba a sani ba ko sakamakon gwajin sauran iyalinsa nasa ya fito.
Tuni jami’ai a birnin Mumbai suka kafa wata alama a kofar gidan tauraron na fina-finan India suna masu cewa “wuri ne da ake kula da shi”.


Mutane da dama sun yi ta yi wa iyalin addu’a a shafukan sada zumunta. Cikinsu har da tauraruwa Sonam K Ahuja da tohon dan wasan kurket na India Irfan Pathan.

Mutane da dama suna yi wa Amitabh Bachchan addu’a….


“Zuwa ga Amitabh ji, ina mai bin sahun al’ummar kasar nan wajen yi maka addu’ar samun sauki da wuri! Kai mutum ne jarumi ga miliyoyin ‘yan kasar nan! Za mu ba ka kulawa ta musamman. Ina yi maka fatan alheri da samun sauki!” a cewar Ministan Lafiya na India Harsh Vardhan.

Labarai Makamanta

Leave a Reply