Kasafin Kudi: ‘Yan Kwangila Na Bin Gwamnatin Tarayya Bashin Biliyan 765

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola, ya bayyana cewa a zaman yanzu haka ‘yan kwangilar da su ka gina titina da gadoji na bin Gwamnati bashin Naira biliyan 765.1.

Ya ce an yi ayyukan ne a manyan titinan gwamnatin tarayya da manyan gadojin da ke kan wa?annan titina.

Ya ce an bayar da naira biliyan 110.5 wajen ayyukan manyan titina domin fara biyan wannan ?imbin bashi da ya bibiyi Gwamantin Tarayya a cikin kasafin 2022.

Fashola ya bayyana haka ne a ranar Talata, lokacin da ya ke kare kasafin 2023 a gaban Kwamitin Majalisar Wakilai ta ?asa mai kula da Ayyuka.

“Ya zuwa watan Oktoba, 2022, Ma’aikatar Ayyuka na da bashin ku?a?en ‘yan kwangila da ba ta biya ba, har na naira 765, 017, 139,752.92, na ayyukan da ake kan yi na cikin kasafin 2022.”

A kan haka sai Fashola ya koka da yadda Najeriya ke kasa ?aukar nauyin gudanar da ayyuka ba tare da ciwo bashi ba, haka kuma ya yi ?orafi dangane da yadda ba a dan?ara wa Ma’aikatar Ayyuka ma?udan ku?a?e a kasafin ku?i.

Ya ce, “ana yi wa ?angaren ayyuka ?wauron ku?i, ta yadda ta kai ana yin kasafin naira miliyan 200 ga ayyukan titunan da za su iya lashe naira biliyan 20 ko sama da haka.”

Related posts

Leave a Comment