Kasafin Kuɗin 2021: Tufka Da Warwara Buhari Ya Yi – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ya kushe kasafin kudin shekara mai zuwa da shugaban kasa ya gabatar a gaban majalisar tarayya.

Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa wasu daga cikin abubuwan da gwamnatin tarayya ta kawo a a kundin kasafin kudin na 2021, sun ci karo da dokokin kasa.

Jagoran adawar kasar ya bukaci shugaban kasa Buhari da mukarrabansa, su je su sake zama a kan kundin kasafin na badi, da nufin ceto tattalin arzikin kasa.

A jiya ranar Juma’a ne Abubakar ya fitar da wani dogon jawabi da ya yi wa take da: “The 2021 Budget Proposal Contravenes The Fiscal Responsibility Act.”
‘Dan takarar shugaban kasan na PDP a 2019 ya yi kira ga shugaban kasa ya yi wa kundin gyare-gyare, ta yadda kasafin ba zai ci karo da dokar batar da kudi ba.

Haka zalika, Atiku Abubakar ya bukaci ayi wa kasafin kudin kasar kwaskwarima ta yadda za a iya shawo kan matsalar tattalin da ke damun Najeriya a halin yanzu.

“Kasafin ya na da gibin Naira tiriliyan 5.21. Wannan kaso ya kai kusan 3.5% na jimillar tattalin arzikin Najeriya a 2019, hakan ya saba da dokar kudi ta 2007.”

Atiku ya kara da cewa sashe na 12 na wannan doka ya ce bai halatta a samu gibin fiye da 3% na karfin GDP a kasafin kudin da za a gabatar a gaban majalisa ba.
“Najeriya ta na GDP na $447b a 2019. 3% na wannan shi ne $13.3, idan aka yi lissafin Dala a kan N379, wannan adadi zai ba ka Naira Tiriliyan 5.07” Don haka ne Atiku ya ce gibin da za a samu a kasafin 2021 ya zarce abin da doka ta yi tanadi.

A makon jiya, mun kawo maku dalla-dallar yadda Najeriya za ta batar da kudin kasafin shekara mai zuwa, inda ake sa ran a batar da Naira tiriliyan 13.08.

Labarai Makamanta

Leave a Reply