Ministar ku?i da kula da tattalin arziki Hajiya Zainab Ahmad ta bayyana abin da aka ware wa ma’aikatun Najeriya a kasafin ku?in Shekarar 2021 da shugaban Kasa ya gabatar a gaban Majalisa.
Ma’aikatar gidaje da ayyuka, lafiya, da tsaro za su samu makudan kudi a badi, Kasafin ku?in ya nuna gwamnatin tarayya ta na shirin kashe Naira tiriliyan 3.85 wajen ayyukan more rayuwa a shekara mai zuwa na 2021.
An ruwaito cewa wadannan makudan kudi da aka ware domin ayyuka, sun zarce abin da aka yi kasafi a shekarar nan, Naira tiriliyan 2.69. 29% na kasafin kudi badi zai tafi ne wajen manyan ayyuka, gwamnatin Najeriya ta ce ta kama hanyar ware wa ayyuka 30% na kasafin kudi.
Ministar tattalin arzikin kudi da kasafi, Zainab Ahmed, ta bayyana wannan a jiya ranar Talata. Babu sabon abu a cikin kasafin kudin da Shugaba Buhari ya gabatar Zainab Ahmed ta ce zuwa watan jiya, gwamnatin shugaba Buhari ta fitar da Naira tiriliyan 1.2 daga cikin kudin ayyuka na shekara mai-ci.
Ahmed ta ce gwamnati za ta maida hankali ne a kan kammala ayyukan da aka riga aka fara, a maimakon kinkimo wasu sababbin kwangiloli.
Kamar yadda Ministar ta yi bayani, an ware wa ma’aikatar gidaje da ayyuka Biliyan 404.64, sai kuma ma’aikatar kudi ta samu Biliyan 382.63. Misis Zainab Ahmed ta ce ma’aikatar sufuri za ta samu Biliyan 256.09 a 2021, daga nan kuma sai ma’aikatar wuta da aka yi kasafin Biliyan 198.2.
Ma’aikatar ilmi za ta samu Biliyan 197.41 domin yin ayyukan more rayuwa. Sauran ma’aikatun da ke gaba-gaba su ne na kiwon lafiya da tsaro. Ministocin harkar ruwa da na kiwon lafiya duk za su samu Biliyan 152.77.
Biliyan 121.2 da 110.2 aka ware wa ma’aikatar aikin gona da ta tsaro. Wata ma’aikata da za ta samu kudi sosai ita ce ta jiragen sama, da aka yi wa kasafin Biliyan 89.