Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar sananniyar Kungiyar na mai rajin kare hakkin ‘yan Najeriya SERAP ta shigar da kara a babban kotun tarayya dake Abuja a kan kasafin kudin 2022.
SERAP na so a hana shugaban kasa Muhammadu Buhari kashe Naira biliyan 22 a shekara mai zuwa a cefanen abinci da zirga-zirga a fadar gwamnati.
Naira biliyan 22 aka warewa fadar shugaban kasa domin alawus, sayen kayan abinci da na jin dadi da tafiye-tafiye a cikin Najeriya da kasashen ketare.
A ranar Juma’ar da ta gabata, kungiyar ta shigar da kara mai lamba FHC/ABJ/CS/1361/2021 a kotun. Har yanzu ba a sa ranar da za a fara yin shari’ar ba.
Kamfanin dillacin labarai na kasa yace Kolawole Oluwadare da wata lauya Adelanke Aremo suka gabatar da wannan kara a gaban kotun tarayya a madadin SERAP. Wannan kungiya ta koka kan yadda gwamnati take cigaba da cin bashin kudi domin a cike gibin da ke cikin kasafin kasar, bayan ta ki rage facakar da take yi.
“A matsawa shugaban kasa ya rage kasafin kudin N26bn da aka warewa fadar shugaban kasa domin tafiye-tafiye, cin abinci da kayan dadi.” Idan an yi haka, kungiyar tana so gwamnatin tarayya ta aikawa majalisar tarayya sabon kundin kasafin kudi wanda yake kunshe da wannan ragin da aka yi.
Bugu da kari, lauyoyin SERAP suna so Alkali ya tursasawa Muhammadu Buhari ya fito da abin da asibitin fadar shugaban kasa ya ci tun daga 2015 har zuwa yau. SERAP tana so a karkatar da wannan N26bn wajen gyara sauran asibitocin kasar.