Karfin Da Soji Ke Amfani Dashi Kan ‘Yan Bindiga Ya Yi Yawa – Dr Gumi

IMG 20240315 WA0034~2

Sanannen malamin addinin musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya ce sojojin Najeriya suna tsawwalawa a hanyar da suke bi wajen yaƙi da ƴan bindiga.

Ya ce hanyar da sojojin ke bi domin kawo ƙarshen ƴan bindigan a yankin Arewacin Najeriya, ta yi tsauri da yawa.

Ya ce dakarun sojoji da na sama sun ƙaddamar da hare-hare ta ƙasa da ta sama da suka hallaka iyalan ƴan bindigan, mata da ƴaƴansu, lamarin da ya harzuƙa su, inda suke ganin hakan a matsayin yaƙi.

Malamin ya bayyana hakan ne a wani shiri a shafin X da jaridar Daily Trust ta shirya. Ya dage da cewa bin hanyar amfani da tattaunawa ce kawai za ta dakatar da ayyukan ƴan bindiga a yankin Arewa.

Akalamansa: “A gare su (sojoji) suna yaƙi ne. Maganar gaskiya sojoji sun tsaurara a kansu, sojojin sama suna kashe iyalansu.” Gumi, wanda a baya ya sha shiga daji domin tattaunawa da ƴan bindiga, ya yi kira da abi hanyar da tsohon shugaban ƙasa, Umaru Musa Yar’adua ya bi ya magance tsagerun Neja-Delta, domin kawo ƙarshen ayyukan ƴan bindiga.

Labarai Makamanta

Leave a Reply