Karayar Arziki: Gwamnatin Tarayya Za Ta Zaftare Albashin Ma’aikata

Ma’aikatar ku?i da kasafi da tsare-tsare ta ce an kafa kwamiti da zai yi nazarin yadda za a rage yawan ku?a?en da gwamnati ke kashewa musamman zabtare albashi da kuma rage yawan hukumomi.

An ambato ministar ku?in Najeriya Zainab Ahmed na cewa, dole ne a fito da hanyoyin warware matsalar ?arancin ku?i da gwamnati ke ciki, lura da irin tsare-tsaren da ta ?auko da kuma lalurorin yau da kullum da ta ke magancewa kamar albashi da sauran ku?a?en tafiyar da gwamnati.

Mai magana da yawun ma’ikatar ku?in ta Najeriya Yunusa Tanko Abdullahi ya shaida wa BBC cewa gwamnati za ta yi aiki da shawarwarin rahoton kwamitin Oronsaye wanda tsohuwar gwamnatin Jonathan ta kafa.

Rahaton Oronsaye ya bayar da shawarar rage yawan hukumomi da ma’aikatu saboda sun yi yawa domin rage yawan ku?a?en da gwamnati ke kashewa.

Shugaban ?asa ya ce a diba a san me za a yi – akwai ma’aikau da yawa da ke biyan albashi da ya fi na wasu ma’aikatu, ana son a tace a raba albashin da wasu suke kar?a ya kasance an ba mutane da yawa maimakon ?an ?alilan,” in ji Yunusa Tanko Abdullahi.

Amma ya ce an kafa kwamitin da zai tantance ya tace hukumomi ko ma’aikatun da za a rage kuma kwamitin zai tura wa shugaban kasa shawarwarinsa daga nan shugaban ya ?auki mataki.

An da?e da aka gabatarwa gwamnatin Najeriya da shawarwarin rahoton kwamitin Oronsaye da aka kafa tun a 2011.

Gwamnati kuma a cewar mai magana da yawun ma’ikatar ku?in Yunusa Tanko Abdullahi “a yanzu an shiga wani yanayi na ?o?arin da gwamnati ke yi na biyan albashi da kyar.”

Annobar korona ta haifar fa?uwar farashin mai da rashin kasuwa wanda ya sa dole gwamnati ta sake lale – kuma kasafin ku?inmu ya samu gi?i,” in ji shi.

Ministar ku?i Zainab Ahmed ta ce gwamnatin tarayya ta aminta da kasafin kudin na kusan naira tiriliyan 14, dogaro da hasashen samun kudin shiga kusan tiriliyan takwas.

Akan haka ta ce mafita ?aya ita ce yanke ku?a?en ayyukan da ba su da muhimmanci sosai, da kuma hade wasu ma’aikatun da wasu, a kuma soke ayyukan da za a iya tafiyar da gwamnati ba tare da su ba.

Ministar ta ce su kansu ma’aikatun da ke da matu?ar muhimmanci akwai bukatar su zauna da ita don duba yiwuwar yanke wani kaso na ku?a?en da suke kashewa.

An kuma ambato ministar na cewa wani abu da ke damunta shi ne akwai ayyukan da duk shekara da ake gani a kasafin ku?i bayan tuni an biya kudaden kammala su, da kuma yadda ake tsula ku?a?e ga wasu ayyukan da ba su da wani tasiri ga talaka.

Related posts

Leave a Comment