Karayar Arziƙin Najeriya: Rashin Iya Shugabancin Buhari Ne – PDP

Jam’iyyar adawa ta PDP ta bayyana cewa rashin sanin aiki ne, irin na shugaba Buhari yasa Najeriya ta tsinci kanta a karo na biyu wajen karayar tattalin arzikin kasar.

Jam’iyyar PDP tace tana kira ga shugaban kasa daya amince da wanan gazawa tasa da yayi, sannan kuma ya bar kwararru wanda suka san kan lamarin su ja ragamar kasar wanda hakanne kawai zai bada damar sake dawo da kasar kan turba na kwarai.

PDP tace shugaba Buhari ne kawai shugaban da aka taba yi da ya jefa Najeriya matsin tattalin arziki har sama da sau 3.

Wannan ya fito ne daga kakakin jam’iyyar PDP, Kola Ologbondiyan.

Ko a kwanakin baya ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyar PDP zaɓen Shekarar 2019 da ya gabata Atiku Abubakar ya fito fili ya soki lamirin Buhari inda ya bayyana sho a matsayin mutum mai kafiya wanda bai ɗaukar shawara, kuma dalilin durƙushewar arziƙin Najeriya kenan inji shi.

Labarai Makamanta