Shahararren Malamin addinin islama kuma shugaban darikar Tijjaniya, Sheik Dahiru Usman Bauchi, a zantawarsa da manema labarai, ya ce za su dauki mataki akan dukkanin gwamnonin da suka hana su yin karatun Allo a Jihohin su.
Idan baku manta ba, a kwanakin baya gamayyar gwamnonin yankin Arewa, sun haramta makarantun allo tare da harmta barace-barace wanda har suka dinga diban almajiran Jihohin su, suna mai dasu garuruwan su na asali.
Haka zalike ya yiwa gwamnatin jihar Kaduna martani, kan amincewa da dokar yin dandaka ga duk mutumin da aka kama da laifin yin fyade, inda Mallam ya ce babu irin wannan hukuncin kwata-kwata a cikin shari’ar Musulunci.