Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana yadda ?an ?asa ke cigaba da nuna ?acin ransu yayin da ?arancin man fetur ke ?ara ?amari a Kaduna, Katsina, Kano
Yayin da karancin man fetur ke kara ta’azzara a fadin Najeriya, masu ababen hawa a jihohin Kaduna, Kano da Katsina na biyan cin hanci don samun man fetur ?in.
Binciken da Wakilan Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya suka yi a jihohi ukun ya nuna bakin ciki da bala’in da ‘yan kasar ke ciki.
NAN ta kuma tattaro cewa galibin manyan ‘yan kasuwa da masu zaman kansu sun rufe gidajen mai.
Haka kuma, ’yan kalilan da ke aiki sun yi watsi da farashin man inda suka kaishu zuwa N800 zuwa N1000, lamarin da ya kara ta’azzara halin da ake ciki.
Hakazalika, an lura da cewa ‘yan kasuwar bakar man fetur, musamman masu safarar mai a gefen hanya sun yi ta kwana, inda ake sayar da galan lita 4 a tsakanin N5000 zuwa N6000.