Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa harkawo yanzu ana jeka ka dawo akan takamaimai ɗin mafi ƙarancin albashi ma’aikata.
Kungiyar kwadago ta bayyana dubu 250,000
a matsayin mafi ƙarancin albashi, a gefe guda Gwamnatin Tarayya ta bayyana dubu 62,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi.
Gwamnoni sun bayyana bazasu iya biyan Naira dubu 60,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ba. Gashi wanki hula na ƙoƙarin kaiwa dare
Kwanakin da kungiyar kwadago ta ɗiba na komawa yajin aiki na karatowa.