Gwamnonin sun bayyana haka ne a sanarwar ƙarshen taro da suka fitar a bayan taron su na ƙasa da suka gudanar a jihar Enugu, da ke kudu maso gabashin Najeriya.
Yayin da suka koka kan tafiyar hawainiyar da tattaunawar gwamnati da ƙungiyar ƙwadago ke yi, gwamnonin sun yi la’akari da cewa matsayar da ƙungiyar ta ɗauka ya dace a halin yanzu ganin irin wahalhalun da ƴan Najeriya ke ciki sakamakon tsadar rayuwa da ake fama da ita.
Sanarwar ta ƙara da cewa ”Yayin da taron gwamnonin ke goyon bayan buƙatar ƙungiyar ƙwadago, dole ne duk wata yarjejeniya ta yi la’akari da albashin da gwamnatocin ƙananan hukumomi da na jihohi za su iya biya”.
”Yayin da ake ci gaba da tattaunawa, muna kira ga dukkan ɓangarori da su kai zuciya nesa, kar a kai ga furuci da kuma ayyukan da za su iya haifar da karya doka, wanda ka iya kai wa ga jefa tattalin arziƙi cikin ruɗani.”
Gwamnonin na PDP sun kuma bayyana takaici kan “yadda tsare-tsaren gwamnatin tarayya ƙarƙashin jam’iyyar APC ke neman gurgunta tartalin arzikin ƙasar.”