Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Karamomi Biyar Na Sabon Shugaban EFCC Muhammad Umar

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a ranar Juma’a ya amince da nadin Muhammad Umar a matsayin mukadashin shugaban hukumar yaki da rashawa ta EFCC.

Hakan ya biyo bayan dakatar da Ibrahim Magu da aka yi a matsayin mukadashin shugaban hukumar yaki da rashawar bisa zargin cin hanci da karkatar da kudade.

Amma galibin mutane ba su san komai game da sabon shugaban riko na hukumar yaki da rashawar ba shiyasa Legit.ng ta kawo muku wasu muhimman abubuwa da ya kamata su sani game da Umar.

  1. Kafin nadinsa a ranar Jumaa, Umar shine direktan sashin ayyuka na hukumar ta EFCC.
  2. Umar shine mutum na biyar da ya rike mukamin shugabancin hukumar ta yaki da rashawa a tarihi.
  3. Sabon shugaban na riko na hukumar EFCC mataimakin kwamishina ne a Rundunar Yan sandan Najeriya, NPF.
  4. Shine jami’i mafi girma a hukumar ta EFCC bayan Ibrahim Magu
  5. Kazalika, an yi wa sabon shugaban rikon na EFCC shaidan riko da addini.

A wani labarin kunji cewa Dakatattacen mukadashin shugaban hukumar yaki da rashawa ta EFCC, Ibrahim Magu da ake bincika a kan zargin rashawa ya nemi IG na Yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya bayar da shi beli.

Kwamiti na musamman da shugaban kasa ya kafa karkashin jagorancin tsohon alkalin kotun koli Ayo Salami ne ke bincikar Magu.

Magu, wanda aka tsare tun ranar Litinin ya rubuta wasika ta hannun lauyansa, Mr Oluwatsosin Ojaomo a ranar Juma’a zuwa ga IG na neman beli kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Tun ranar da aka kama shi, Magu yana tsare ne a wani wurin ajiya na rundunar ‘yan sanda a Abuja inda daga nan ya ke zuwa gurfana gaban kwamitin binciken.

Wasikar da lauyansa ya rubuta zuwa ga ofishin IGP mai dauke da kwanan wata na 10 ga watan Yuli kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito ta nemi a bayar da shi beli, “bisa sanayar da aka masa a kasa.”

Exit mobile version