Gwamnatin jihar Kano da ha?in gwiwar hukumar hana ta’amulli da fataucin miyagun kwayoyi na ?asa za ta yi wa dukkan ?an takara a za?en ?ananan hukumomi da ke tafe a jihar gwajin kwayoyi.
Za a yi zaben kananan jihohin na Kano ne a watan Janairun shekarar 2021.
Kwamishinan kananan hukumomi, Alhaji Murtala Sule Garo ne ya sanar da hakan yayin bude wani taron wayar da kai na kwana 2 da aka shirya wa ma’aikatan kananan hukumomi 44 a jihar don wayar da su game da illolin miyagun kwayoyi.
Garo, wanda ya wakilci gwamnan jihar, Dakta Abdullahi Ganduje wurin taron ya bayyana cewa za a yi irin gwajin ga dukkan ma’aikatan ?ananan hukumomi 44 a jihar.
Ya ce dukkan wadanda aka samu da miyagun ?wayoyi a jikinsu za a tura su cibiyar sauya halaye.