Kano: Za A Koma Biyan Karancin Albashi Na Dubu 18

Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Jihar Abdullahi Umar Ganduje ta sanar da daina biyan ma’aikatanta karancin albashin N30,000 tare da gaggauta komawa biyan karancin albashin zuwa N18,000 kamar yadda aka saba kuma aka gada.

Gwamnatin ta bayyana cewa hakan ya biyo bayan karayar tattalin arzikin da aka shiga saboda Covid-19 Annobar ta yi mummunar illa ga tattalin arzikin jihohi da dama na Najeriya ballantana jihar Kano.

A yayin tabbatar da wannan sauyin mai magana da yawun Gwamna Umaru Ganduje, Salihu Tanko-Yakasai, ya ce halin da kasar nan ta shiga sakamakon annobar korona ce ta saka hakan.

Tanko Yakasai Ya ce: “Gwamnatin jihar ta koma biyan tsohon karancin albashi saboda halin da ta shiga. Abinda muke samu a matsayin gwamnati yanzu ya ragu kuma ba za mu iya cigaba da biyan N30,000 ba a matsayin karancin albashin.”

Amma kuma, ma’aikatan gwamnatin da ke jihar sun jajanta yadda gwamnatin jihar bata bada wata sanarwa ba kafin ta fara zabtare musu albashi, sai dai suka wayi gari da ganin giɓi a Albashin nasu.

Labarai Makamanta

Leave a Reply