Kano Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙaramar Hukuma Ya Mutu

Allah ya yi wa zababen shugaban karamar hukumar Bebeji a Jihar Kano, Alhaji Ali Namadi rasuwa Marigayin ya rasu ne misalain karfe daya na daren Litinin kwanaki biyu bayan hukumar zabe ta tabbatar masa da nasararsa.

Za a yi jana’izarasa a garinsu na Bebeji yau Talata kamar yadda mai magana da yawun tawagar yakin neman zabensa, Ibrahim Tiga ya sanar.

“Ali Namadi, wanda ya lashe zaben ranar Asabar na karamar hukumar Bebeji a Jihar Kano, ya riga mu gidan gaskiya ne bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Namadi ya rasu ne a ranar Talata misalin karfe daya na dare a cewa mai magana da yawun ofishin yakin neman zabensa, Ibrahim Tiga.

An sanar da rasuwarsa a safiyar ranar Talata, kwanaki biyu bayan hukumar zabe ta jihar ta tabbatar da nasararsa. Kawo yanzu ba a sanar da sanadin mutuwarsa ba.

Namadi na cikin jerin ‘yan takarar karamar hukuma na APC da suka yi nasara a zaben da aka kammala na kananan hukumomi a ranar 16 ga watan Janairun 2021 wadda har yanzu suna jirar rantsarwa.

Labarai Makamanta

Leave a Reply