Labarin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewar wani mummunan hadarin mota yayi sanadin mutuwar wasu malaman addinin Islama shida a yau
Malaman sun rasu ne a kan hanyarsu ta komawa Kano daga karamar hukumar Sumaila bayan sun kammala aikin da’awah a karkashin gidaunyar Imam Malik.
Wata ma’aikaciyar gidauniyar ta shaida ma jaridar Daily Nigerian cewa da misalin karfe 3 na yammaci suka sami labarin hadarin.
Ta ce hadarin ya rutsa da dukkan malamai shida, wadanda jagororin aikin da’awa ne a jihar.