Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta damke wani magidanci mai suna Auwalu Kabaki, mazaunin kwatas ta Mariri da ke karamar hukumar Kumbotso ta jihar.
Ana zargin Auwalu da laifin garkame matarsa na tsawon kwanaki a cikin gida duk da tsohon cikin da take da shi, har ta Mutu.
An ruwaito daga makwabtan wanda ake zargin cewa, bayan wari ya ishesu na kwanaki ne mazauna yankin suka kira ‘yan sanda. Bayan shiga gidan da aka yi ne aka ga gawar matar mai juna biyu wacce ake zargin ta rasu ne yayin nakuda, don kuwa cikinta ya isa haihuwa.
Wata makwabciyar mamaciyar wacce ta bukaci a rufe sunanta, ta ce “Babu wanda zai iya bayyana abinda ya shiga tsakanin ma’auratan. “Saboda tun bayan dawowarsu Unguwar, ba su shiga jama’a. hatta almajirai baka taba ganin suna tsaya a kofar gidan suna bara,” cewar makwabciyar.
Firdausi Isah Musa, ‘yar uwar mamaciyar, ta sanar da manema labarai cewa, tun bayan da suka yi aure, marigayiyar ‘yar uwarta bata taba samun jin dadi ba. Hakan ne yasa damuwa tayi mata yawa.
“Kusan shekarunsu takwas da aure kuma Allah ya albarkacesu da ‘ya’ya uku amma ‘yar uwata ta kasance kullum cikin tsaka mai wuya. “Mijinta ya saba garkameta a gida. Baya barinta ta yi mu’amala da kowa hatta ‘yan uwanta. An kai ga lokacin da damuwa ta yi mata mugun yawa,”.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda yace an fara bincike don gano yadda al’amarin yake.