Kano: Uwargida Ta Yanka Amarya Dab Da Aure

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar da kama wata matar aure mai suna Suwaiba Shuaibu a kan zarginta da kashe budurwar mijinta mai suna Aisha Kabir ta hanyar dadda?a mata wuka ana sauran kwanaki kadan aurenta da mijinta mai suna Alhaji Sharri Ali dake kauyen Gimawa ?aramar Hukumar Doguwa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Talata, ya ce an nemi amaryar an rasa amma daga baya sai aka ga gawarta a wani kango.

“A ranar 2 ga watan Janairu wurin karfe 10:30 na safe mun samu labarain ganin gawar Aisha Kabir daga kauyen Gimawa a wani kango.
“Ana zargin an soka mata wuka ne a wuya. Mun ziyarci wurin inda muka dauki gawarta zuwa babban asibitin Tudun Wada wanda likita ya dubata.

“Kwamishinan ‘yan sanda CP Habu A. Sani ya bukaci jami’an tsaro da su nemo wadanda suka yi aika-aikar. “A wannan halin ne aka damko Suwaiba Shuaibu mai shekaru 20.

Bincike ya nuna cewa mijinta ya kashe shekaru 6 suna soyayya da budurwar kuma za su yi aure.”
Kiyawa ya ce wacce ake zargin ta amsa laifinta. Ta ce da kanta ta kira budurwar mijinta sannan ta kaita kangon ta soka mata wuka a wuya, kirji da sauran sassan jikinta.

Ya ce an mika lamarin hannun sashin bincike na musamman kan kisan kai kuma za a mika wacce ake zargin a gaban kotu.

Related posts

Leave a Comment