Kano: Tinubu Ya Gwangaje Kannywood Da Kyautar Miliyan 50

Labarin dake shigo mana daga jihar Kano na bayyana cewar Bola Ahmed Tinubu, ‘dan takarar kujerar shugabancin kasa na jam’iyyar APC a zaben 2023 ya gwangwaje masana’antar Kannywood da gudumawar N50 miliyan domin cigaban masana’antar.

Mujallar fim ta ruwaito cewa, Tinubu ya bayar da wannan makudan kudaden ne a yayin da ya halarci taro na musamman da ‘yan fim suka hada masa a daren Lahadi a fadar gwamnatin jihar Kano.

A yayin jawabi kan manufar taron, Furodusa Abdul Amart Maikwashewa ya ce: “Wannan taron na matasan fim ne masu goyon bayan Tinubu. Sun shirya shi a karkashin gidauniyar Kannywood don su nuna yadda karfin goyon bayan da yake da shi a wurin ‘yan fim.

“A saboda haka a shirye muke domin bashi dukkan goyon baya don ganin ya kai ga nasara.”

A jawabin shugaban kungiyar masu shirya fina-finai ta Najeriya, MOPPAN na kasa, Dakta Ahmad Sarari, ya sanar da cewa Kannywood a matsayin babbar masana’antar da ke kawo kudin shiga da aikin yi ga matasa. Don haka yayi kira ga Tinubu da ya duba yadda masana’antar take idan ya samu cin zabe.

Yayin mayar da martani, Gwamna Samuel Lalong, shugaban kwamitin yakin neman zaben Tinubu na kasa ya sanar da su cewa daman suna cikin tafiyar dumu-dumu. Hakazalika, ya sanar da gudumawar naira miliyan hamsin da Tinubu ya bai wa masana’antar domin inganta ta.

Labarai Makamanta

Leave a Reply