Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewa shugaban majalisar malaman addini na Jihar Sheikh Ibrahim Khalil ya yi kira da babbar murya ga Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf cewa a yi gaggawar naɗa Jarumar Tik-Tok Murja Kunya mukami na mai ba Gwamna Shawara.
Sheikh Khalil yace ko shakka babu nada Murja muƙamin zai taimaka gaya wajen karfafa tarbiyyar Matasa musanman Mata a faɗin Jihar.
Ina Kira Ga Gwamnatin Kano Ta Bawa ‘Yar Mu Murja Kunya SA Ko SSA Yadda Za Ta Shiryar Da Matasa Kuma Gwamna Zai Samu Lada, Cewar Sheikh Ibrahim Khalil
Shugaban Majalisar Malamai ta Kano Sheikh Ibrahim Khalil ya roƙi gwamnatin jihar ta yi karatun ta nutsu kan sha’anin Murja Ibrahim Kunya.