An bayyana aikin rusau da Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ke yi a fadin jihar da cewa abu ne wanda ya dace kuma ya ke bisa ka’ida.
Ɗan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Albasu Honorabul Musa Haruna Tahir ne ya bayyana hakan a yayin wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a Kaduna.
Honorabul Musa Tahir ya ƙara da cewar duk wanda ya ke bibiyar siyasar Kano a lokacin yakin neman zaben da ya gabata ya sani domin tun a lokacin yaƙin neman zabe Gwamna Abba ya fadi cewar idan ya yi nasarar zama gwamna zai tabbatar da cewa ya kawar gami da rushe duk wani gini da aka yi wanda ba ya bisa ka’ida a jihar.
“Ina tabbatar muku da cewa mai girma Gwamna aikin rusau da ya ke bisa ka’ida ya ke, kuma dukkannin masu fahimtar gaskiya sun san da haka shi ya sa da yawa ba su yarda sun shiga kwamacalar gine-ginen ba”
Ɗan Majalisar wanda ya ke a zangon farko na zuwa majalisa ya bayyana aniyar da ya ke da ita na kawo cigaba ga ƙaramar Hukumar Albasu da jihar Kano gaba daya.