Lamarin ya faru ne a jiya bayan mamakon ruwan sama da aka yi.
Ginin wanda na kasa ne, ya rufto ne yayin da mutanen gidan suke bacci inda ya danne ‘yan gidan gaba dayansu su 18, inda aka yi nasarar ceton ransu daga makota da kuma jami’an hukumar kashe gobara ta kano. Nan take mutum biyu suka mutu, inda ragowar kuma suka jikkata aka garzaya da su asibiti domin ba su kulawa.
Wanan ba shine na farko ba da aka samu rufatawar gini a cikin Kano. Ko a kwanakin bayan wasu ‘yan mata biyu sun mutu bayan da gini ya rufto musu a unguwar Jakara da kuma wasu yara biyu su ma da suka rasa ransu bayan ruftowar gini a unguwar Warure duka a jihar Kano.