Kano Pillars Ta Lallasa Lobi Stars Ci 3 Da Nema

Kano Pillars ta yi nasara a kan Lobi Stars da ci 3-0 a wasan mako na 31 da suka fafata a gasar Firimiya ta Najeriya a jihar Kaduna, Najeriya.

Pillars din ta ci kwallon farko ta hannun Umar Hassan tun kan hutu, sannan David Ebuka ya kara na biyu, sai Rabi Ali da ya ci na uku.

Da wannan sakamakon Pillars ta hada maki 55 tana ta biyu a kan teburi, bayan buga wasa 31 a gasar bana.

Har yanzu Akwa United tana mataki na daya a kan teburi da maki 57, bayan da ta buga wasa ba ci a gidan Plateau United a ranar ta Lahadi.

Pillars da ake kira masu gida za ta ziyarci Sunshine Stars a wasan gaba na mako na 32, ita kuwa Akwa karawa mai zafi za ta yi a gida da Enyimba International.

Wasu sakamakon wasannin da aka buga ranar Lahadi:

  • Warri Wolves 2 – 0 Abia Warriors
  • Katsina United 3 – 0 Ifeanyi Ubah
  • Kada City 2 – 0 Enugu Rangers International
  • Adamawa United 1 – 1 Mountain Of Fire And Miracles
  • Wikki Tourists 2 – 1 Dakkada
  • Plateau United 0 – 0 Akwa United
  • Enyimba International 1 – 1 Rivers United

Labarai Makamanta

Leave a Reply