Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Kano: Matashi Ya Kashe Abokinshi Saboda Budurwa

Rahotanni daga Jihar Kano sun bayyana cewa wani abun tashin hankali ya afku a Unguwar Sheka da ke karamar hukumar Kumbotso na jihar Kano.

Mutanen wannan yanki dai sun tashi da alhini na mutuwar wani dan unguwar mai suna Sagir Muhammad, wanda ake zargin wani matashi mai suna Abdullahi Muhammad da kashe shi.

Ana dai zargin Abdullahi da kashe Sagir Muhammad, dan kimanin shekara 22 ta hanyar dukansa, sakamakon sabani da ya shiga tsakaninsu a kan wata budurwa, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

An tattaro cewa wani idon shaida da ya nemi a boye sunansa ya bayyana cewa rigima ce ta auku a tsakanin matasan biyu a kan wata budurwa da ke unguwar.

Majiyar ta ce bayan da lamarin ya faru an dangana da marigayin zuwa wata karamar cibiyar lafiya da ke unguwar ta Sheka inda kuma a nan ne rai ya yi halinsa.

Kakakin rundunar yan sandan ihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce yanzu haka suna gudanar da bincike a kai.

Exit mobile version