Hukumar kare hakkin dan adam a jihar Kano ta ce cikin watanni tara sun karbi bayanan aikata fyade har 721 daga sassan jihar.
Shugaban hukumar ya shaida wa BBC cewa cibiyar da ke lura da wadanda aka yi wa fyade da sauran nau’ukan cin zarafin mata mai suna WARAKA ce ta tantance tare da bin diddigin al’amarin.
Fyaɗe, matsala ce da ke ƙara ƙamari a Najeriya musamman yadda ake cin zarafin mata da kananan yara ta hanyar fyaden.
Cibiyar WARAKA ta karbi korafin aikata fyade da sauran nau’ukan cin zarafin mata fiye da dari-bakwai, daga watan Janairu zuwa watan Satumbar shekarar nan.
Hukumar kare hakkin ɗan’adam ta jihar Kano tana aiki kafada-da-kafada da cibiyar ta WARAKA tsawon lokaci kasancewar ta mamba a kwamitin gudanarwar cibiyar.