Kano: Mafusata Sun Yi Wa Ɗan Majalisa Dukan Tsiya

Dan Majalisar Tarayya ya sha da kyar a hannun Mafusatan Matasan Mazabarsa a Kano saboda yawan daukar Alkawari babu cikawa

Dan majalisar tarayya mai wakiltar Dawakin Tofa da Rimin Gado dake jihar Kano, Tijjani Abdulkadir Jobe ya sha da kyar a hannun wasu fusatattun matasa a mazabarsa bayan sun zarge shi da yawan fada babu cikawa.

Majiyarmu ta rawaito cewa lamarin ya auku ne a ranar Lahadin da ta gabata a lokacin da Honarabul Jobe ya je kaddamar da wani aiki a kauyen Gulu dake karamar hukumar Rimin Gado.

A halin yanzu dai ɗan Majalisar na kwance a wani asibiti yana jinyar raunukan da ya samu sakamakon dukan da matasan suka yi mishi.

Labarai Makamanta

Leave a Reply