Kano: Kwamishinan ‘Yan Sanda Ya Yabawa Masu Zanga-zanga

Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kano ya abawa masu Zanga-zangar kawo karshen matsalar tsaro A Arewa.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta yaba wa masu zanga-zangar neman daƙile matsalar tsaro bisa aiwatar da ita cikin lumana.

Kwamishinan ‘Yan Sanda Habu Ahmad ne ya tarɓi masu zanga-zangar, inda suka miƙa masa buƙatunsu a rubuce.

Kwamishinan ya karɓi buƙatun nasu tare da tabbatar musu da cewa za a miƙa buƙatun nasu ga hukumomin da suka dace.

An shiga rana ta biyu kenan da Gamayyar Kungiyoyin Arewa suka kira yin Zanga-zangar gama gari a fadin Arewa, domin kawo karshen yawaitar kashe-kashen da ke faruwa a yankin.

Labarai Makamanta

Leave a Reply