Kano: Kotu Ta Yi Watsi Da Bukatar Rimin Gado

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewar a ranar Talata ne Babbar Kotun Tarayya a Jihar ta yi fatali da buƙatar da dakataccen Shugaban Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin-hanci da Rashawa ta Jihar Kano, Muhuyi Magaji Rimingado.

A roƙon da ya shigar gaban kotun, Riminga ya nemi kotun da ta hana kwamitin bincike da majalisar dokoki ta Kano ta kafa, da kuma hana ƴan sanda su bincike shi, tsare shi ko yi masa barazana.

Sannan ya roƙi kotun da ta bada umarnin kowa ya dakata ba tare da ɗaukar mataki kan takardun shaidar lafiya na biyu da a ke zargin yayi amfani da su.

Da ta ke yanke ƙwarya-ƙwaryan hukunci Mai Shari’a Jane Inyang, ta ce kwamitin bincike da aka kafa da kuma jami’an tsaro suna da iko da doka ta basu na su binciki Rimingado.

Inyang ta kuma yanke cewa babu hurumi na jaddada ko yin watsi da hukuncin da kotu mai hurumi iri ɗaya ta yi da wacce a ka miƙa wa ƙorafi ta yi.

Ta kuma ce kamata ya yi Rimingado ya shigar da ƙorafi a kan yan majalisar dokoki a Babbar Kotun Jiha ba ta taraiya ba.

Labarai Makamanta

Leave a Reply