Kano: Kotu Ta Tabbatar Da RiminGado A Halastaccen Shugaban Hukumar Yaki Da Rashawa

Kotun masana’antu ta kasa dake Abuja ta tabbatar da shugaban hukumar yaki da rasha ta jihar Kano (PCACC), Muhuyi Magaji, wanda aka dakatar a matsayin Shugaban hukumar, Kotun ta umarci gwamnatin jihar Kano da ta biya Magaji albashinsa da alawus din da ta rike masa bayan dakatar da shi a watan Yulin shekarar da ta gabata.

An dakatar da shi na tsawon wata daya a watan Yulin 2021 bisa rashin amincewa amsar wani akawun hukuma daga ofishin akawu-janar na jihar. Kotun ta ayyana cewa har yanzu Magaji yana nan a matsayin shugaban hukumar yaki da rashawa ta jihar tare da umartar Abdullahi Ganduje ya cigaba da biyansa albashinsa da alawus na N5,713,891.22.

Yayin gabatar da shari’ar a ranar Laraba, Alkali Oyebia Oyewumi, ya ce Magaji yana da alhakin a biyasa albashinsa duk karshen wata daga ranar da aka kammala shari’a zuwa lokacin da za’a maido da shi bakin aikinsa. Sai dai, alkalin ya ki amsar bukatar Magaji na ayyana dakatar da shi a matsayin abun da bai dace ba gami da soke shi.

Kotun ta ce, gwamnati na da damar dakatar da shi, kuma yin hakan zai iya ko kin bashi damar jin ba’asin dakatar da shi, dalili kuwa shine dakatarwa ba tauye hakki bane na dindindin, ba kamar kora ba wacce ke bama wanda aka dauka aiki jin ba’asi.

Haka zalika, kotun ta dora laifi ga rundunar ‘yan sandan jihar Kano bisa kama Magaji ba tare da lasisin kama mutum, wacce bata bayyana wani laifi ba, inda kotun take ganin hakan ba daidai bane a shari’ance, sannan ta hana kwamishinan ‘yan sandan wanda yake jeri na shida cikin wadanda ake kara daga shiga lamarin wanda yayi karar a kowanne abu da ya shafi wajen aikinsa.

Har zuwa yanzu, gwamnatin jihar Kano ba tayi martani game da lamarin ba, yayin da a safiyar Juma’a aka yi kokarin tuntubar wayar kakakin gwamnatin jihar, Muhammad Garba don jin ta bakinsa bata shiga ba.

Labarai Makamanta

Leave a Reply