Tsohon hadimin na Ganduje Salihu Tanko Yakasai ne ya wallafa labarin barinsa kasar a shafinsa na Twitter tare da yin hamdala kan haka, da bayyana cewar zai dawo bayan Buhari ya sauka daga mulki.
Ganduje ya kori Salihu Tanko Yakasai a watan Fabrairu bayan ya soki gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari kan gazawarta wajen shawo kan matsalar tsaro da ke addabar Najeriya musamman yankin Arewacin kasar.
Daga nan ne kuma sai jami’an tsaron farin kaya (DSS) suka damke Yakasai wanda aka tsare na tsawon kwanaki a wata magar?ama a birnin tarayya Abuja.
A wasu hotuna da ya saka a shafin sada zumunta, an ga Yakasai a filin jirgin saman wata kasar da bai bayyana sunanta ba saboda dalilan tsaro.
An kuma ga jirgin saman kasar Qatar a bayan hoton. Ya rubuta a shafinsa na Twitter “Sai wata rana Naija! Alhamdulillah!”.
A wani labarin, Salihu Tanko Yakasai, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari yana ruda ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda a kasar nan da wa’adin da yake basu tare da jan kunne.
Yakasai, wanda Ganduje ya kora a watan da ya gabata saboda kalubalantar mulkin Buhari da jam’iyyarsa ta APC, ya sanar da hakan ne a ranar Asabar.