Hukumar Karota ta jihar Kano karkashin jagorancin shugaban Hukumar Hon.Dr. Bappah Babbba ‘Dan Agundi, ta yi nasarar cafke wata katuwar mota kirar Kwantena makare da giya a cikinta.
Hukumar ta yi nasarar cafke motar ne a daren jiya Lahadi bayan wata doguwar ja-in-ja da jami’an suka sha da masu motar giya, kafin su yi nasarar kawo ta zuwa hedikwatar hukumar dake Sani Marshall Road.
Da yake jawabi a madadin Shugaban Hukumar Karota, Mataimakin na musamman ga Gwamnan Kano, kan Karota Hon Nasiru Zico, ya ce “za a mika wannan motar ne zuwa hannun Hukumar Hisbah ta jihar Kano.