?aya daga cikin mutanen da suka ragewa ?an mazan jiya da suka yi gwagwarmaya domin ?antar da talaka daga ?angin bauta, cin zali, musgunawa da noman gandu, biyan haraji da jangali Alhaji Muhammadu Dauda ?angalan ya amsa ?iran mahalicci a jiya Asabar.
Tuni aka yi jana’izar sa da misalin ?arfe biyar na yammacin jiya a gidansa dake unguwar Fagge a birnin Kano.
Marigayin ya bayyana a wata shira da jaridar Daily trust cewar ya fara siyasa yana ?an shekaru 21 a duniya kuma dalilin shigarsa siyasa shine saboda ana zalintar talaka, ana saka shi yin aiki mai wahala da noman gandu, an mayar dashi bawa ana cutar dashi da hefa shi a cikin matsi.
An ta?a ?aure shi yayi watanni shida a gidan yarin Kurmawa a lokacin gidan yarin an yi shine domin horo da saka mutane a cikin damuwa, yace da aka tashi fa?a masa laifinsa kawai ance yana ?o?arin tunzura talakawa su yiwa masu sarauta bore.
Yace manyan abokan siyasarsa sune Musan Musawa, Shehu Shatatima, Sani Darma, Adamu Danjaji, Malam Aminu Kano, Salihi Iliyasu, Garba Muhammad Gumel, Tanko Yakasai, Magaji ?anbatta, Babba ?an Agundi.
Shine mutumin da ya zagaya Gusau, Tsafe, ?auran Namoda, Maradun da sauran garuruwa domin nemowa NEPU magoya baya kuma ya bayyana cewar lallai zagayen da yayi ya samu darussa da sanin garuruwa da al’umma kuma an samu nasarar da ta kamata.
Ya ce shi sana’ar ?inki ya ha?a da siyasa kuma ta rufa masa asiri sosai ta taimaka masa wajen yin harkokinsa yadda ya kamata.
Marigayi Aminu Kano shine mutumin da ya fi bashi gudunmawa tare da koyon abubuwa na ha?uri, juriya, tsayawa akan manufa, gaskiya da jure azaba ko ba?ar wahala domin a ?arshe a cimma burin da aka saka a gaba. Yace shi kam Alhamdu lillah a wajensa ?walliya ta biya ku?in sabulu domin a kowanne mataki na mu?ami a ?asar nan yanzu ?a?an talakawa ne suka kai.
A wani taro da aka ta?a gudanarwa na ?an mazan jiya da taron Talakawa Summit a Jigawa yace shi kam babu abinda zai ce da Alhaji Sule Lamido sai godiya da fatan alheri bayan ya sake fitowa da manufa da a?idun NEPU/PRP kuma yayi aiyyukan da kowa yake alfahari dasu, yace yana taka muhimmiyar rawa wajen tallafa min ni da iyali na.
Allah ya ji?an Dattijo Alhaji Dauda ?angalan ya gafarta masa kurakurensa, ya albarkaci bayansa.