Kano: Jam’iyyar APC Ta Dare Gida Biyu

An samu mummunar ?araka ta rikicin cikin gida a cikin jam’iyya mai mulki ta APC a Jihar Kano, inda wani tsagin jam’iyyar APC a jihar a karkashin jagorancin Hussaini Isa Mairiga, ya sanar da sauke shugabannin tsagin jam’iyyar a karkashin jagorancin Abdullahi Abbas na hannun daman Gwamna Ganduje.

An sake zaben shugabannin tsagin jam’iyyar APC da ke karkashin jagorancin Abbas a shekarar 2018 saboda rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar a shekarar 2017.

?angaren da Abbas ya ke jagoranta shine mai daurin gindin gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar ganduje, kuma wanda uwar jam’iyya ta ?asa ta san da zaman su.

Da ya ke magana da manema labarai a ranar Alhamis, Mairiga ya ce Abbas da sauran mukarabbansa sun karbi shugabancin APC ne ta barauniyar hanya, ta hanyar zaben da ya raba kan mambobin jam’iyya.

“Ta hanyar zaben bogi Abdullahi Abbas ya zama shugaban jam’iyya, amma duk da hakan, ya gaza tabuka komai bayan mulkin kama karya.

“Ba halastattun shugabanni bane, shugabancinsu ya sabawa kundin tsarin mulkin jam’iyya, a saboda haka duk wani abu da ya fito ta karkashinsu haramtacce ne. “Abinda na ke nufi a nan shine; duk wani dan takarar a zaben kananan hukumomi da za’a yi a watan Janairu kar ya sayi fom din takara ta hannun haramtattun shugabanni.

“Duk Wanda ya shiga takara ta hannunsu ya shiga asara don ko ya ci zabe sai an kwace a kotu,” a cewarsa.

A karshe Mairiga ya bukaci shugabancin APC na kasa ya kafa kwamitin riko na jam’iyyar a jihar Kano domin ya gudanar da sabon zaben shugabanni na gaskiya.

Hukumar zabe ta jihar Kano (KANSIEC) ta tsayar da ranar 16 ga watan Janairu a matsayin ranar zaben kananan hukumomi a fa?in jihar.

Related posts

Leave a Comment