Shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai, Hon. Alhassan Ado Doguwa, ya ce har yanzu shi dan jam’iyyar APC ne kuma bai da wani dalili na barin jam’iyyar imma a yanzu ko a nan gaba.
Ya ce wadanda ke zargin yana shirin sauya sheka daga jam’iyyar suna yada labaran karya ne kawai wanda ba su da tushe ballantana makama.
Ado Doguwa, wanda ke wakiltan mazabar Doguwa/Tudun Wada ta jihar Kano a majalisar wakilai, ya bayyana hakan ne lokacin da ya kai ziyarar ban girma ga Tinubu a Abuja a ranar Lahadi.
Shugaban masu rinjayen ya samu rakiyar dan majalisar jihar da ciyamomi biyu daga mazabarsa da kuma sauran manyan shugabanni daga jihar.
Da yake ba Tinubu tabbacin samun goyon bayansa da kuma ci gaba da kasancewa a APC, ya ce gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje na a hannu nagari.
Tinubu ya mika godiya ga Ado Doguwa kan wannan ziyara da ya kai masa, yana mai alkawarin kasancewa tare da shi da mutanen jihar kan goyon bayansu.