Shugaban Hukumar tace fina-finai da daba’i ta Jahar Kano Malam Ismail Na’abba Afakallahu ya sha alwashin tsaftace fina-finan da ake saki ta YouTube.
A yayin ziyararmu ga shugaban hukumar mun tattauna muhimman batutuwa wadanda suka shafi masana’antar shirya fina-finai.
Malam Afakallahu mutumin kirki mai karamci da haba-haba yana da sakin jiki da tarairayar Bako yayi matukar godiya bisa ga shawarwarinmu musamman aniyarmu ta ganin an tsaftace fina-finai an kuma inganta su tun daga tushen su. Mun yi nazarin hana fim ba zai zamo mafita ba, domin zamani ya zo da fasaha da kimiya iri-iri wanda kallo ba zai dakilu ba.
Maimakon haka mun shawarci hukuma da ta inganta fina-finai su zamo masu fadakarwa, wa’azantarwa, ilmantarwa da wayar da kan al’umma ta fannonin rayuwa da dama. Akwai mutanen da ba za su iya saurarar wa’azi ba, amma ta kallon fim sai su sami ilmi da fadakarwa mai yawa kuma ta amfanar da su, mun kuma bayyanawa hukuma wasu shawarwari game da abubuwan da ya dace a dauki mataki game da sha’anin gyaran tarbiyyar al’umma.
Da yake bayani Malam Afakallahu ya bayyana irin nasarori da cigaban da hukumarsa ta samar karkashin gwamman Kano Dr Abdulllahi Umar Ganduje wanda jama’a da dama ba su san da su ba. Hakika wannan nasarori da Malam Afakallhu ya samar sun isa Maigirma Gwamna Ganduje yayi alfahari ko bayan saukarsa a mulki.
Musamman tsaftace sha’anin sha’irai na yabon Manzon Allah S.A.W wanda ake samun kusa-kurai na wuce gona da iri, da kuma bijiro da tsarin tantance jarumai ta hanyar yi musu rijista, wanda hakan ya kara tsaftace jaruman ya farfado da su daga baccinsu cewa akwai doka da oda a Kano, kuma duk wanda yayi wasa da Doka dole tayi aiki a kansa, kamar misalin Jarumi Adam A. Zango da ya ki baiwa Hukuma hadin kai kuma doka tayi aikinta a kansa, wanda daga bisani da kansa ya janye ra’ayinsa ya zo yayi mubayi’a ga Hukuma.
Daga kyakkyawar niyyarsa ta samar da gyara da kuma tsaftace tarbiyar al’umar Kano da Arewa baki daya, Malam Afakallahu ya bayyana yadda ya bijiro da tsarin tsaftace abubuwan da ake saki a YouTube. Duk da dai wasu sun fahimci wannan lamari a baibai.
Hakan na da alaqa da yadda da aka koma cin kasuwar fina-finai ta Manhajar YouTube wanda akan sami fina-finai masu cike da kusa-kurai masu barazana ga tarbiyya. Hakan ya saka Malam Afakallahu jajircewa wajen ganin an dakile wannan matsala, kuma tuni gwamnatin Kano ta tabbatar da wannan kuduri a hukumance. Daga yanzu duk mai saka fina-finansa a YouTube muddin zai yi mu’amala da Kano dole yayi rijista da hukuma a dinga tace fina-finansa.
Hakika wannan babban alkhairi ne da cigaba wanda tarihi ba zai manta shi ba, bayan wannan akwai cigaba da nasarori da dama da ya bayyana mana amma lokaci ba zai ba ni hadin kai na bayyana muku ba.
Bayan nan, mun tattauna lamarin Aqidar addini, musamman yanzu da jahar Kano ke fuskantar babban Kalubalen wasu mutane da ke cin mutuncin Annabi S.A.W matansa da sahabbansa masu karyata Alqur’ani da maganganun manzo S.A.W ingantattu, (Wal’iyyazubillah) duk da yake Hukumarsa ba ta da hurumi game da hakan amma ya ba da tabbacin cewa zai yi duk mai yuyuwa wajen ganin gwamnatin Kano ta dauki mataki akan wannan matsala.