Kano: Hukumar Tace Fina-Finai Ta Bada Umarnin Rufe Gidajen Gala

IMG 20240310 WA0423

Hukumar tace Fina-finai da Ɗab’i ta Jihar Kano ta umarci rufe dukkan gidajen gala a fadin jihar. Shugaban hukumar a jihar, Abba El-Mustapha shi ya bayyana haka a ranar Lahadi 10 ga watan Maris a shafinsa na Facebook.

Abba ya ce an dauki wannan matakin ne saboda shirye-shiryen da ake yi na tukarar watan azumin Ramadan.

Daukar matakin ya biyo bayan wata ganawa da shugaban hukumar ya yi da jagororin kungiyar masu gidajen gala da ke jihar. El-Mustapha ya ce dokar za ta fara aiki ne daga ranar Lahadi 10 ga watan Maris har zuwa ranar bikin sallah.

Shugaban hukumar ya gargadi masu gidajen gala da su guji karya doka domin duk wanda ya saba zai fuskanci hukunci mai tasiri. Ya ce daga cikin matakan da za su dauka shi ne kwace lasisin gidajen galar na din-din-din ga duk wanda ya saba dokar.

Abbaya ce kofarsu a bude take ga duk mai wani korafi ko kuma shawara kan wata matsala da ke faruwa.

Labarai Makamanta

Leave a Reply